Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya bayyana cewa, an yi bincike mai tsanani kan dukkan jiragen sama da za su tashi zuwa Amurka a filin jiragen saman na Beirut, da kuma haramtawa fasinjojin dake dauke da Visan kasashen Syria, Iraki, Iran, Yemen, Libya, Sudan da kuma Somaliya shiga jiragen sama.
Wasu kafofin watsa labarum kasar ma sun ba da labarin cewa, a daren ranar 28 ga wata, filin jiragen sama na Paris na kasar Faransa, ya hana wani iyalin Syria da ya iso birnin daga Beirut zuwa birnin Atlanta na kasar Amurka, an kuma mayar da iyalin zuwa Lebanon. Daga baya, an fara aiwatar da wannan umurni a filin jiragen saman Beirut. (Bilkisu)