A cewar ofishin bada agaji na MDD OCHA, daga cikin matsalolin aikin kai agajin 100 da aka samu a watan Nuwamba, kashi 66 cikin 100 ya shafi cin zarafin jami'an aikin bada agaji ne ko kuma kayayyakin agajin, yayin da kashi 26 cikin 100 ya shafi matsaloli ne game da tsare tsaren kai agajin, biyar daga ciki ya shafi batun yin katsalandan ne game da yadda ma'aikatan ke tafiyar da ayyukansu, bakwai kuma ya shafi yadda ake aza haraji ba bisa ka'ida ba, sannan biyu daga ciki ya shafi yadda ake kwace aikin rabon agajin daga hannun jami'an da abin ya shafa.