in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun aikawa daukacin Sinawa gaisuwar bikin bazara
2017-01-26 19:43:15 cri
A yau ne a madadin kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikawa daukacin Sinawa da ke babban yankin kasar Sin da yankunan musamman na Hong Kong da Macoa da Taiwan da ma Sinawa da ke sassan daban-daban na duniya gaisuwar bikin bazara.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kana babban kwamandan rundunar sojojin kasar, ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da aka shirya a babban dakin taron jama'a da ke nan birnin Beijing.

Za a fara bikin bazara na bana ne a ranar 28 ga wannan wata da muke ciki. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China