Guterres ya bayyana ta hoton bidiyo cewa, shekarar Zakara wata alama ce da ke bude wani sabon babi ga ci gaban rayuwar bil-Adama. Kana tana jaddada muhimmancin kuzari da sadaukar da kai da nuna akidar mayar da hankali ga aiki.
Babban sakataren MDDr ya bayyana cewa, wadannan akidoji za su yi mana jagora yayin da muka shiga wata matsala. Ya kuma bayyana shekara ta 2017 a matsayin shekara ta zaman lafiya. Saboda haka,wajibi ne mu hada kai don magance aukuwar tashin hankali, take hakkin bil-Adama, yaki da talauci da sauran matsaloli.(Ibrahim)