Jakada Zhou Pingjian ya ce, bara shekaru 45 ke nan da kulla dangantakar diflomasiya tsakanin Sin da Najeriya, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara kasar Sin, kuma hadin-gwiwar kasashen biyu ta zurfafa. Zhou ya ce, kwanan baya, ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya kai wani rangadin aiki Najeriya, inda a madadin gwamnatocin kasashen biyu, ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka fitar da wata sanarwa dangane da martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, lamarin da ya aza tushe ga kara habaka huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Najeriya.
A wani labarin kuma, jakada Zhou ya ce, ofisoshin jakadancin Sin dake Najeriya za su ci gaba da himmatuwa wajen kare hakkin Sinawa dake Najeriya, ta hanyar samar musu wani yanayi mai kyau na gudanar da harkokinsu a Najeriya.(Murtala Zhang)