Kwamandan hukumar mai kula da shiyyar arewa maso yammacin Najeriya Shehu Umar ya shaidawa manema labarai cewa, daga cikin wannan adadi 187 maza, kana 272 kuma mata.
Ya ce, a wannan shekarar da muke ciki, hukumar ta fara ilimantar da jama'a game da illolin safarar mutane gami da matakan yadda za su kare kansu daga fadawa wannan tarko.
Kwamandan ya ce, rashin kudi, ita ce babbar matsalar da hukumar ta fuskanta a shekarar da ta gabata. (Ibrahim)