Da ta ke jawabi yayin bikin ranar yaki da fasakauri ta duniya, ministar ta ce gwamnati za ta bullo da wata kafa ta tattara bayanai daga sassa da ma'aikatu daban-daban, domin toshe kafofin da kudaden gwamnati ke zurarewa.
Ministar ta kuma jadadda muhimmancin amfani da bayanai wajen kare iyakokin kasar.
A cewarta, musayar bayanai tsakanin ma'aikatu abu ne da ya zama tilas, duba da muhimmancinsa wajen hana zurarewar dukiyar gwamnati.
Kemi Adeosun wadda ta ce ana nan ana kokarin kaddamar da kafa daya tilo da za a rika tattara bayanai daga ma'aikatu da hukumomi daban-daban, ta ce wannan babban ci gaba ne ga kasar, domin kuwa abu ne mai wahala tabbatar da dukkan ma'aikatu sun hada hannu tare da mai da hankali wajen tattara bayanai a wuri guda tare da amfani da shi. (Fa'iza Mustapha)