Kwamandan dakarun da ke yaki da mayakan Boko Haram a jihar ta Borno Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai cewa, kimanin mutane 100 ne suka mutu ciki har da sojoji 2, da ma'aikatan bayar da agaji 2 baya ga wasu fafaren hula da dama da suka jikkata.
Ya ce, lamarin ya faru ne bayan da dakarun saman kasar suka samu bayanan asiri cewa mayakan Boko Haram suna kokarin sake hallara a yankin.
Tuni dai rundunar sojojin saman kasar ta tura jirgi mai saukar ungulu zuwa wurin da lamarin ya faru don kwashe mutanen da suka ji rauni. A hannu guda kuma gwamnatin jihar Borno ta umarci dukkan asibitocin gwamnati da ke yankin da su samar da magani kyauta ga mutanen da suka jikkata sanadiyar wannan hari.
Shugaba Buhari ya yi alkawarin taimakawa gwamnatin jihar Borno don kula da wadanda wannan hari bisa kuskure ya rutsa da su. Haka kuma ya bukaci jama'a da su kwantar da hankalinsu, duba da yadda dakarun kasar ke daf da kawar da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar baki daya. (Ibrahim)