in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a horar da matasa dubu dari biyu kan inganta harkokin noma a Nijeriya
2017-01-21 13:54:28 cri

Wani Jami'i ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, karkashin kashin farko na shirin inganta harkokin noma wato Agricultural Transformatin Support Program ATASP-1 a takaice, gwamnatin kasar ta yanke shawarar horar da matasa dubu dari biyu kan dabarun renon iri, sarrafawa da kuma alkinta shi.

Shugaban shirin na kasa Haruna Akwashiki, ya bayyana a Abuja babban birnin kasar cewa, za a fara bada horon ne daga makon farko na watan Fabrairu.

Haruna Akwashiki, ya ce manufar shirin ita ce, cike gibi dake akwai wajen samar da iri da samar da aikin yi da kuma samun riba kan albarkatun gona da suka hada da shinkafa da dawa da rogo.

Ya kara da cewa, kashin farko na shirin ya kunshi matakai uku da suka hada da, samar da kayayyakin aiki, bunkasa ribar albarkatun gona da kuma tabbatar da shirin na tafiya yadda ya kamata.

Har ila yau, ya ce za a aiwatar da shirin ne cikin shekaru biyar a kananan hukumomi sittin na jihohin Enugu, Anambra da Niger da Sokoto da kuma Jigawa.

Haruna Akwashiki ya ce gwamnatin kasar da bankin raya kasashen Afrika AFDB ne, za su samar da kudaden aiwatar da shirin, inda bankin zai bada dala miliyan dari da hamsin da biyu yayin da gwamnatin za ta bada dala miliyan ashirin da uku.

A shekarar 2015 ne aka kaddamar da shirin na ATASP na daya, a wani bangare na kokarin gwamnatin Tarayyar Nijeriya na baza komar tattalin arzikinta a fannin noma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China