Mr. Lu Kang, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin da yake amsa tambayoyi game da ziyarar da shugaban kasar Amurka Barack Obama zai kai birnin Hiroshima na kasar ta Japan, ya kara da cewa yakin duniya na biyu ya bayyanawa al'ummar duniya darasi daga tarihi, game da muhimmancin hana sake aukuwar irin wadannan yake-yake, da tabbatar da zaman lafiya a duniya bisa dokokin da aka kafa bayan yakin.
Ya ce Sin tana fatan Japan za ta shirya ziyarar shugabannin sauran kasashen duniya a Hiroshima ne, bisa tushen kauracewa ci gaba da bin ra'ayin nuna karfin soja, wadda ta taba kawo babbar illa ga jama'ar kasar ta Japan, da ma jama'ar nahiyar Asiya da na duniya gaba daya. (Zainab)