A cikin jawabinsa a wani taro a dakin taron jama'ar kasar a nan birnin Beijing da safiyar wannan rana, shugaba Xi ya nuna farin cikinsa bisa ga kokarin zurfafa kwaskwarima, cigaba da inganta dokoki a shekarar data gabata.
Ya yi alkawarin kara azamar inganta aiki a jam'iyyar kwaminis ta kasar mai mulki da kuma gwamnatin har ma da samar da karin arziki, karin ababen amfanar al'umma da kuma martaba ga kasar.
Dangane da matsowar bikin bazarar wanda yake da muhimmancin kwarai a haduwar iyali baki daya a kasar, shugaban ya jaddada muhimancin zumuncin 'yan uwantaka da kuma samar da ilimi ga iyali.
Yace al'adun Sinawa da muhimmancin dake tattare da haduwar iyali da kuma kaunar juna ba abin da za'a manta dashi bane, don ganin yara sun girma cikin koshin lafiya tsoffi kuma sun samu kula mai kyau.(Fatimah)