in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata a sanya siyasa a batun TPP ba
2016-11-22 20:26:37 cri
A kwanan baya ne, Mr. Donald Trump mai jiran gadon shugabancin kasar Amurka ya ce, da zarar ya hau mukamin shugabancin kasar, kasar ta Amurka za ta janye daga yarjejeniyar cinikayyar da ke tsakanminta da kasashen yankin Fasifik wato TPP.

Mr. Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyanawa taron manema labarai a yau matsayin kasar Sin game da batun TPP cewa, a lokacin da ake kokarin kakkafa yankunan cinikayya cikin 'yanci a Asiya da tekun Pasifik, bai kamata a sanya siyasa a irin wannan shiri ba.

Wasu kafofin yada labaru na ketare suna ganin cewa, idan kasar Amurka ta janye daga TPP, "yarjejeniyar dangantakar abokantaka a fannonin tattalin arziki a shiyya-shiyya", wato RCEP a Turance, wadda kasar Sin ke shugabanta, za ta samu ci gaba matuka. Game da irin wannan magunguna, Mr. Geng Shuang ya nuna cewa, kungiyar kawancen Asean ce ke shugabantar wannan yarjejeniya ta RCEP. An dauki lokaci mai tsawo, kasar Sin da kungiyar Asean da sauran bangarorin da abin ya shafa suna kokarin ciyar da shawarwarin RCEP gaba. Bangaren Sin yana son ci gaba da hada kan bangarori daban daban don ciyar da shawarwarin gaba a kokarin ganin an samun kyakkyawan sakamako cikin hanzari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China