Kungiyar tarayyar Afrika AU ta baiwa matan Afrika 5 lambar yabo wadanda suka yi fice a fannin kimiyya karkashin shirin lambar yabo ta shekara shekara na AU ta Kwame Nkrumah na matan Afrika.
An gudanar da bikin ne a lokacin taron kolin mambobin kungiyar AU karo na 28 a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.
Ita dai kyautar lambar yabon ta Kwame Nkrumah ta kimiyya ana bayar da ita ne ga mutanen da suka yi fice a fannin kimiyya a yankuna da shiyyoyi a fadin nahiyar ta Afrika. A cewar AU, wannan lambar yabo za ta karawa mata azama wajen shiga a dama dasu a fannin cigaban kimiyya da fasaha a nahiyar.
Matan da suka samu kyautar ta wannan karon sun hada da yankunan gabashi, arewaci, kudanci, da kuma yammacin Afrika, matan su ne; Jane Catherine Ngila daga kasar Kenya, shiyyar gabashin Afrika, matar ta yi fice ne a fannin nazarin kimiyyar muhalli da tattalin albarkatun ruwa.
Sai Lamia Chaari Fourati daga kasar Tunisia, shiyyar arewacin Afrika, ta samu lambar yabonta ne sabo da fice a fannin fasahar sadarwa.
Sai shiyyar Afrika ta kudu inda Celia Abolnik daga kasar Afrika ta Kudu ta yi fice a fannin gano kwayoyin cututukan da suka shafi numfashi, musamman game da cututukan tsuntsaye da kiwon jimina a Afrika.
Sai kuma wasu matan biyu daga shiyyar yammacin Afrika su ne: Rokia Sanogo daga Mali, kwararriya a fannin kimiyyar hada magungunan gargajiya, da kuma Olu-Owolabi Bamidele daga Najeriya, wacce ta kware a fannin cigaban sinadaren samar da ruwa mai tsabta.(Ahmad Fagam)