Kasar Ghana ta bayyana niyyar cimma burin kawar da mutuwar mata masu juna biyu nan da shekarar 2057, in ji kwamitin tsarin iyali da ci gaba na kasar (NDPC) a ranar Alhamis. A cikin wani jawabin da ya bayar a birnin Accra, darekta janar na NDPC, Nii Moi Thompson, ya bayyana cewa, wannan makasudi zai kasance cikin tsarin ci gaba bisa tsawon lokaci na kasar Ghana yadda ya kamata.
Shekarar 2057, shekara ce da za ta kasance ta cikon shekaru 100 da kafuwar kasar Ghana. Mun sanar da cewa, ba za mu samu mutuwar mata masu juna biyu ko guda ba a shekarar nan.
A kasar Ghana, adadin uwaye matan dake matuwa a lokacin da suke da juna biyu ya kai kashi 144 cikin 100.000, a yayin da ake hasashen wata raguwar wannan adadi a ko ina cikin duniya bisa wani matsakaici na mutuwar mata 70 cikin mata 100.000.
Akwai mutanen da suke bayyana cewa, wannan zai yi wuyar aikatawa, amma ba kawai wani batu ne na kididdiga ba, in ji mista Thompson.
Muna mayar da burin kawar da mutuwar mata masu juna biyu a matsayin wani batu na tunani, in ji jami'in NDPC. (Maman Ada)