Wata sanarwa da ofishin watsa labarai na majalisar ya fitar, ta bayyana cewa, Madam Meuller za ta maye gurbin Kyung-wha Kang 'yar kasar Koriya ta kudu wadda a halin yanzu take rike da mukamin shugabar tawagar shirin mika mulki a ofishin babban sakataren MDD.
Mueller tana da kwarewar aiki a harkokin ci gaban kudi da na kasashen duniya na sama da shekaru 20. A watan Sataumban shekarar 2014, Madan Mueller ta rike mukamin darektar rukunin bankin duniya inda ta yi aiki a fannonin da suka shafi tsara dabaru, manufofi da kasafin kudi da kuma shirye-shiryen da aka son aiwatarwa a shekarar 2016 wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 62 .
Haka kuma jami'ar ta yi aiki a matsayin mai shiga tsakani da nufin karfa hadin gwiwa tsakanin bankin duniya da MDD.(Ibrahim)