A jiya Talata, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya zabo karin mutane goma daga yankunan kasar daban-daban da yake son nadawa ministoci.
Idan majalisar dokokin kasar ta amince da nadin na su, za su yi aiki a matsayin wakilan shugaban kasa a yankuna goma dake kasar, inda tuni aka mika sunayensu ga majalisar don neman sahalewarta.
Yayin wani taron manema labarai, Akufo-Addo ya ce yana da tabbacin mutane da ya zaba, za su tabbatar da samar da nagartacciyar gwamnatin da ba a taba samun irinta ba a tarihin kasar.
Kawo yanzu, shugaban ya zabi mutane talatin da shida da yake son nadawa ministocin bangarori daban-daban, inda yanzu haka majalisar dokokin kasar ke aikin tantance su. (Fa'iza Mustapha)