in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Ghana ta alkawarta samar da kudade domin bunkasa hada hada a sassa masu zaman kan su
2017-01-24 09:34:27 cri
Gwamnatin kasar Ghana ta alkawarta samar da makudan kudade, domin bunkasa hada hadar cinikayya ga sassa masu zaman kan su.

A cewar mutumin da ake sa ran zai rike mukamin minista a ma'aikatar cinikayyar kasar Kwadwo Kyerematen, sabuwar gwamnatin ta Ghana, na da nufin maida hankali ga inganta ayyukan sassa masu zaman kan su, a wani mataki na kawo sauyi ga masana'antun kasar.

Mr. Kyerematen ya kara da cewa, za a samarwa wannan fanni kudade na bunkasa hada hada cikin matsakaici da lokaci mai tsawo.

A watan Disambar bara ne dai jam'iyyar NPP ta lashe zaben kasar da ya gabata, kafin hakan kuwa, jam'iyyar ta alkawarta gina masana'anta guda a ko wace gunduma, lokacin da take tsaka da yakin neman zaben ta.

Game da hakan, Kyerematen ya ce samar da tallafin kudaden fadada hada hadar cinikayya ga masana'antu masu zaman kan su, wani bangare ne na alkawarin da suka yi wa al'ummar kasar. Ya ce wadannan kudade za su ragewa kanana da matsakaitan masana'antu, irin wahalhalu da suke fuskanta yayin neman rance daga bankuna.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China