in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana Akufo-Addo ya mika kashi na biyu na sunayen ministoci ga majalisar dokoki
2017-01-12 10:02:30 cri

A jiya Laraba shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya gabatarwa majalisar dokokin kasar sunayen mutane 12 da yake son nada su ministoci domin neman amincewar majalisar.

Kawo yanzu sunayen da shugaban kasar ya mikawa majalisar dokokin kasar domin nada su ministoci ya kai 25, shugaban na Ghana ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi.

Daga cikin sabbin sunayen da shugaban kasar ya gabatar, har da wata sabuwar ma'aikata da aka kirkiro wadda za ta dinga duba yadda ayyukan sauran ma'aikatun gwamnati ke gudana.

Har ila yau, shugaba Akufo-Addo ya kirkiro ma'aikatar da za ta dinga kula da tsara yankuna da kuma bunkasa cigaba, wanda Dan Kwaku Botwe zai shugabance ta, mutumin ya kasance dan majalisar dokokin kasar ne wanda ke da matukar kwarewa a harkokin majalisa, zai dinga bibiyar yadda tsarin shugabanci a kasar ke gudana.

Akufo-Addo ya shedawa 'yan jaridu a fadar gwamnatin kasar dake Accra cewa, za su yi kokarin kafa gwamnatin al'umma wadanda za su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China