in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka wasu 'yan Ghana su 11 a kan iyakar Togo
2017-01-10 09:54:31 cri
Rahotanni da Ghana na cewa an hallaka wasu 'yan kasar su 11, a wani wuri dake kusa da kan iyakar kasar da arewacin Togo. An ce mutanen wadanda aka harbe da bindiga kana kuma aka fille musu kawuna, na dauke da katunan shaidar 'yan kasa da na kada kuri'u na kasar Ghana.

Ana dai zaton mutanen sun gamu da ajalinsu ne, sakamakon ayyukan masu fataucin mutane, kuma alamu na nuna cewa 'yan asalin arewacin Ghana ne dake yunkurin komawa gida daga tarayyar Najeriya.

Tuni dai aka mika gawawwakin mutanen zuwa dakin ajiye matattu dake garin Kara na kasar Togo, yayin da kuma 'yan sandan yankin suka bukaci 'yan asalin kasar Ghana mazauna yankunan Chereponi, da Bunkprugu, da Saboba, da su je garin na Kara domin duba wadannan gawawwaki, a wani mataki na yunkurin tantance su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China