Shugaban kasar wanda ya sha rantsuwar kama aiki a ranar Asabar din da ta gabata, ya sanar da wannan mataki ne a lokacin taron manema labarai a fadar gwamnatin dake Accra.
Sunayen mutanen sun hada da wadanda suke da kwarewar aiki da kuma sabbi, cikin wadanda ke yin biyayya ga jamiyyar NPP, har ma da wadanda suka shiga jam'iyyar ba da jimawa ba.
Tsohon ministan kudi na kasar Yaw Osafo-Maafo, wanda ke jagorantar kwamitin shirye-shiryen mika mulki, an nada shi a matsayin babban minista wanda zai sa ido ga dukkan ministocin kasar.
Sabbin ministocin na dakon amincewar majalisar dokokin kasar ne bayan kwamitin majalisar ya kammala yin muhawara da kuma tantace su.
Shugaban kasar Akufo-Addo ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta hanzarta amincewa da sunayen ministocin domin kafa gwamnati, don tunkarar dunbun matsalolin da kasar ke fuskanta, da kuma daukar matakan saukakawa game da wahalhalun da 'yan Ghana ke fama dashi. (Ahmad Fagam)