in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Janyewar Burundi daga ICC ba ya nufin kasar zata yi biris da 'yancin dan adam
2016-12-04 13:32:59 cri
'Yan majalisun Burundi sun sanar da janyewar Burundi daga yarjejeniyar Roma ta kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) cewa ba ya nufin cewa kasar ba zata girmama 'yancin dan adam ba, amma zata yi haka bisa girmama 'yancinta.

Game da janyewar Burundi daga ICC, wannan ba ya nufin cewa Burundi ta dakatar da ayyukanta a cikin kasar. Burundi za ta cigaba da yin aiki tare da kungiyoyin 'yancin dan Adam bisa girmama 'yancinta, in ji Alexis Badian Ndayihimbaze, kakakin shugaban majalisar dokokin Burundi a ranar Asabar kwanaki biyu bayan tambayoyin da majalisar ta aikewa ministar shari'a da kuma ministan dake kula da harkokin 'yancin dan Adam kan wani rahoton kungiyar kare 'yancin dan Adam ta kasa kasa (FIDH) dake nuna yiyuwar wani shirin kisan kare dangi a Burundi.

Mista Ndayihimbaze ya bayyana cewa masu hannu kan wannan rahoto sun zargi Burundi da janyewa daga wannan kotu domin kada a tuhume ta kan ayyukan cikin zarafin dan adam da wannan rahoto ya ambato tare da wannan kisan kare dangi.

A cewarsa, rahoton na zargin hukumomin Burundi da rarraba wayoyin salula ga shugabannin al'ummomi domin saukaka gudanar da ayyukan kisan kare dangi da kuma rarraba adduna bisa manufa guda.

'Yan majalisun na kare kansu ta bakin kakakin shugaban majalisar dokokin kasar Burundi cewa, wadannan wayoyin salula na saukaka harkokin sadarwa ta fuskar tsaro a dukkan fadin kasar, kuma game da addunan da ake zance, fiye da kashi 90 cikin 100 na manoman Burundi suna amfani da adduna a matsayin wani kayan aiki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China