in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi ta yi watsi da rahoton kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa
2016-11-18 12:01:17 cri

Mahukuntan kasar Burundi sun yi watsi da wani rahoto da kungiyar nan mai rajin kare hakkin bil Adama ta FIDH ta fitar, wanda ke cewa akwai yiwuwar aikata kisan kiyashi a kasar.

A cewar Willy Nyamitwe, wanda babban mashawarci ne ga shugaba Pierre Nkurunziza na Burundi, rahoton na FIDH na cike da karairayi marasa tushe. Koda yake a daya bangaren ya amince cewa, wasu 'yan kasar da dama sun rasa rayukan su, yayin tashe tashen hankula da suka barke cikin watan Afrilun bara, amma ya danganta hakan da ayyukan 'yan adawa, da kuma wasu kungiyoyi na masu tada kayar baya.

Mr. Nyamitwe ya kara da cewa rahoton na FIDH ya ma kare gwamnatin kasar mai mulki, wadda ya nuna cewa tana dakile yunkurin da ake yi na baiwa matasa horo domin su yaki al'ummar kasar su.

Rahoton dai na kungiyar FIDH wanda aka wallafa a birnin Faris na kasar Faransa, ya fayyace yadda rikicin siyasa ya barke a kasar Burundi cikin watan Afirilun shekarar bara, biyowa bayan bukatar zarcewar shugaba Pierre Nkurunziza kan karagar mulkin kasar a karo na uku, lamarin da ya haddasa kisan mutane sama da 1,000, baya ga wasu mutanen da yawan su ka iya kaiwa 300 zuwa 800 da suka bace.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China