in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
2016: MUHIMMAN ABUBUWA DA SUKA AUKU A DUNIYAR WASANNI
2017-01-26 15:18:06 cri

Zaben shugabancin FIFA

A cikin wannan shekara ta 2016 ne aka zabi Gianni Infantino, a matsayin sabon shugaban hukumar kwallon kafar duniya FIFA. Infantino dan shekaru 45 daga kasar Switzerland, shi ne mutum na biyu daga wannan kasa da zai jagoranci FIFA bayan Sepp Blatter. Ya kuma samu nasara kan abokan takarar sa Sheik Salman daga Bahrain, da Yarima Ali na Jordan, da kuma Kerome Champagne na Faransa.

Yanzu haka dai Infantino ne zai kasance shugaban FIFA na 9 bisa zangon mulki na shekaru 4, bayan saukar Sepp Blatter mai shekaru 79 a duniya, wanda rikita-rikitar cin hanci da rashawa ta yi awon gaba da kujerar sa.

Kafin dai zaben na Infantino, hukumar FIFA ta zartas da wasu kudurori na gyaran huska ga hukumar, a wani mataki na bada damar ci gaba da gudanar da ayyukan ta a bude. Wadannan sauye sauye dai sun kunshi kayyade shekarun shugabancin ta, inda yanzu shugaban FIFA ke da ikon rike wannan mukami karo 3 kacal.

Na'ura ta dole bil'adama a wasan GO

A shekarar ta bara ne kuma manhajar Google mai suna AlphaGo, ta doke kwararren dan wasan daran nan dan asalin kasar koriya ta kudu mai suna Lee SE-dol, bayan da manhajar ta kwamfuta ta lashe wasanni 4 cikin 5 da suka kara. Wannan ne dai karon farko da wata na'ura ta lashe wannan wasa lokacin karawa da kwararru daga jinsin bil'adama. 'yan wasan biyu dai sun kara ne tsakanin ranekun 9 zuwa 15 ga watan Maris, inda daga karshe aka sallamawa manhajar ta AlphaGO. Wasan dara na GO wasa ne da can asali ake yin sa kan allo, ya kuma samo asali ne daga kasar Sin shekaru kusan 2500 da suka gabata. An ce wasan yana daya daga wasannin dara mafiya sarkakiya, da wahalar bugawa a tsakanin wasanni na duniya.

Kobe Bryant ya yi murabus daga wasa

Dan wasan kwallon Kwando Kobe Bryant ya yi ritaya daga wasan ajin kwararru na NBA, a ranar 13 ga watan Afrilu, bayan da kungiyar sa ta Los Angeles Lakers ta lashe wasan karshe da suka buga da Utah Jazz da maki 60.

Bryant ya lashe kofunan NBA 5, da na gasar MVP, da lambar zinari 2 a gasar Olympics. Yana kuma cikin 'yan wasan All star 18 mafiya kwarewa. Dan wasan ya yi bikin ban kwana da wasan kwallon Kwando a ranar 24 a watan Yuni a birnin Beijing na kasar Sin.

Leicester FC ya lashe gasar Firimiyar Ingila

A karon farko a tarihin ta, kungiyar Leicester FC ta lashe kofin firimiyar kasar Ingila. An dai sha mamaki matuka, game da yadda kungiyar da aka kafa shekaru 132 da suka gabata, ta rika doke manyan kungiyoyin kwallon kafar Ingila da suka jima suna taka rawar gani a wannan gasa, kafin daga bisani ta dauke kofin na firimiyar 2016.

Rasuwar Muhammad Ali

A ranar 4 ga watan Yunin shekarar ta 2016 ne zakaran damben duniya Muhammad Ali ya koma ga mahaliccin sa, yana da shekaru 74 a duniya, bayan ya sha fama da cutar makyarkyata tsawon shekaru 32.

Ali ya lashe kambin damben Boxing ajin masu nauyi har karo 3, tsakanin shekarun 1964 zuwa 1978. Ana kuma kallon sa a matsayin wani sadauki cikin 'yan wasan motsa jiki da suka rayu a karni na 20. Baya ga kasancewar sa gwarzo a fagen dambe, Ali ya yi yaki da cutar Parkinson, da kuma ra'ayin nuna wariyar launin fata a Amurka a tsawon shekarun da ya kwashe yana dambe. Shi ne mutum na karshe da ya daga fitilar gasar Olympics ta 2016 kafin kaddamar da gasar ta birnin Atlanta.

Portugal ta lashe kofin nahiyar turai

A karon farko a tarihin ta, kasar Portugal ta lashe kofin nahiyar turai na 2016, bayan da ta doke mai masaukin bakin gasar wato kasar Faransa da ci 1 mai ban haushi. Kafin lashe kofin dai sai da dan wasan da kungiyar kasar ke ji da shi, kuma kyaftin din ta Cristiano Ronaldo, ya fice daga fili sakamakon ciwon da ya ji a gwiwar sa cikin minti na 25. A dai gasar ta 2016, yawan kasashe mahalarta sun karu daga 16 zuwa 24.

Rasha: Danbarwar shan kwayoyin kara kuzari

'Yan wasan motsa jiki na kasar Rasha sun shiga tsaka mai wuya, bayan da kwamitin shirya gasar Olympics IOC ya dakatar da daukacin 'yan wasan kasar, daga halartar gasar birnin Rio da aka yi a Brazil.

Gabanin hakan dai a watan Yukin na bara, wani marubuci, kuma lauya dan kasar Canada mai suna Richard McLaren, ya fidda wani rahoto na bincike, bayan da hukumar dake yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta bukaci hakan, inda ya bayyana cewa kimanin 'yan wasan Rasha 1000, na da hannu cikin laifuka daban daban masu alaka da shan irin wadannan kwayoyi.

Duk dai da cewa Rasha ta karyata wannan rahoto, IOC din ta zartas da hukuncin da ta yanke, kaza lika shugaban ta Thomas Bach, ya yi barazanar kakaba takunkumi na tsawon rayuwa, ga duk dan wasan da aka kama yana karya dokar hana shan irin wadannan kwayoyi.

A daya bangaren kuma IOC ta ce za ta sake yiwa daukacin 'yan wasa 254 da suka shiga gasar Olympics ta Sochi a shekarar 2014 gwaji. A kuma watan Satumbar da ta shude ne wani mai fallasa bayanai, ya fidda wasu alkaluma, wadanda ke nuna cewa, da yawa daga 'yan wasan motsa jiki hadda na Amurka, na amfani da wasu haramtattun kwayoyi a matsayin magani, da amincewar likitoci.

An kara wasanni 5 cikin gasar Olympics da za a yi a Tokyo

Kwamitin shirya gasar Olympic IOC, ya ayyana kara wasanni 5 cikin wasannin da za a rika gabatarwa yayin gasannin da yake shiryawa, tun daga gasar birnin Tokyo da za a yi a shekarar 2020. Wasannin da aka kara dai sun hada da Karate, da wasan hawan tsauni, da tseren ruwa, da tsere kan allo ko Skateboarding. Sai kuma baseball da Softball.

An gudanar da wasannin Olympics karon farko a nahiyar kudancin Amurka

A shekarar ta bara ne aka gudanar da gasar Olympics ta masu lafiya da masu bukata ta musamman karon farko a nahiyar kudancin Amurka. An dai yi gasar ne a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. An kuma bude ta ranar 21 ga watan Agusta. A kuma wannan karo ne aka fara shigar da tawagar 'yan gudun hijira cikin wannan gasa.

Kaza lika a wannan gasa ne dan wasan linkaya Michael Phelps, ya daga lambar yabo karo na 28, ciki hadda lambobin zinari 23 da ya taba samu. Har wa yau shi ma Usain Bolt ya lashe lambobin zinari 3 a karo uku a jere a wannan gasa ta Olympics.

Amurka ita ce ke kan gaba da lambobin zinari mafi yawa a gasar ta bara, sai kuma kasashen Birtaniya, da Sin dake biye a matsayi na 2 da na 3. Kasar Sin ita ce ke matsayi na 2 a yawan lambobin yabo, wadanda yawan su ya kai 70.

A gasar masu bukata ta musamman da aka gudanar tsakanin 7 zuwa 18 ga watan na Satumba, Sin ta yi fintinkau da yawan lambobin zinari a wannan fanni, inda ta samu lambobin zinari mafiya yawa a karo na 4 a jere.

Hadarin jirgin saman kasar Colombia

Wani jirgin saman fasinja dauke da 'yan kungiyar Chapecoense ta kasar Brazil, ya yi hadari a wani tsauni dake kasar Colombia, lamarin da ya sabbaba rasuwar 'yan wasa da jami'an kungiyar 71. Tawagar kungiyar dai na kan hanyar ta ne zuwa buga wasan karshe tare da Atletico Nacional ta Medellin, a gasar cin kofin kungiyoyin nahiyar wato Copa Sudamericana.

Bisa bukatar kungiyar Atletico Nacional, hukumar dake shirya gasar ta nahiyar kudancin Amurka, ta mika kofin ga Chapecoense domin tausaya mata bisa asarar da ta yi. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China