in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rohr ya yi barazanar ajiye Ighalo muddin dan wasan ya koma China
2017-01-18 15:49:33 cri
Babban kocin kungiyar kwallon Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr, ya gargadi fitaccen dan wasan kungiyar Odion Ighalo, da cewa muddin ya yarda ya koma Sin, zai rasa gurbin sa a babbar kungiyar wasan kwallon kafar Najeriya.

Rohr, ya furta hakan ne a lokacin zantawa da manema labarai, jim kadan kafin tashi zuwa wasannin gasar cin kofin kasashen Afrika da ake yi a kasar Gabon, inda zai yi zamo daya daga kwararrun mai sharhi, sakamakon rashin nasarar da kasar ta samu a wasannin share fagen shiga gasar.

An ce Ighalo, yana cikin wani yunkuri na komawa kasar Sin cikin wannan wata na Janairu, inda yake neman sauya sheka zuwa Shanghai Shenhua, bayan da tuni ya nuna sha'awar komawar ta sa.

Rohr ya ce ba shi da tabbas na ko Ighalo zai koma Sin din ko a'a. Amma idan yana da sha'awar komawa lallai yana da zabin yin hakan, sai dai zai yi hasarar gurbinsa na dan wasan gaba a tawagar Super Eagles da zarar ya koma.

"Muna da matashi (Victor) Osimhen wanda a halin yanzu yake a Bundesliga, tun a farkon watan January a Wolfsburg, kuma zan nemo shi" in ji Rohr.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China