Dan wasan mai shekaru 51 a duniya, ya kasance na 2 cikin matakin karshe da nisan kilomita 786 na tseren motocin da aka yi, wanda aka fara daga garin Rio Cuarto ya zuwa garin Buenos Aires. Wannan sakamako dai ya tabbatar da zamansa a matsayi na farko bisa daukacin tsawon lokacin da ya kwashe na sa'o'i 28 da mintuna 49 gami da dakikoki 30.
A nasa bangaren, Loeb ya zama na biyu, bisa karin wasu mituna 5 da dakikoki 13 da ya kwashe. Yayin da Cyril Despres, wanda shi ma yana cikin kungiyar motocin kamfanin na Peugeot, ya kasance na 3 a gasar. (Bello Wang)