Assis ya bayyana cewa, Ronaldinho mai shekaru 36 da haihuwa, na fatan bugawa daya daga kulaflikan da ke buga gasar Copa Libertadores kwallo ne. Cikin su kuwa akwai Chapecoense ko Coritiba na Brazil, ko kuma kungiyar Nacional ta Uruguay.
A wata zantawa da ya yi da jaridar kasar Uruguay mai suna El Pais, Assis ya ce "burin mu shi ne ya buga wasa a wannan shekara ta 2017. Bayan hutu na shekara guda, wanda ya ba mu damar kewaya duniya muka kuma kara fahimtar kasashe da a baya bamu taba sani ba".
Game da yiwuwar bugawa kungiyar Nacional wasa, Assis ya ce a madadin Ronaldinho, sun zanta da wakilan kungiyar, ko da yake ba a kai ga daddale wani kuduri ba tukuna.
Ronaldinho dai ya sha hutu tun bayan da ya rabu da kungiyar Fluminense ta Brazil a watan Satumbar bara. Sai dai a lokacin da yake hutun, ya taba halartar wasu bukukuwa a Peru, da Ecuador, da Guatemala, da Amurka da kuma Sin. Ya kuma halarci gasar futsal da aka buga a kasar India.