in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na yi galaba a kan Ingila cikin watanni 6 – Ibrahimovic
2017-01-18 15:50:14 cri
Mai tsaron bayan kungiyar wasan kwallon kafan Manchester United Zlatan Ibrahimovic, yana jin cewar tamkar ya gama da Ingila ne a kakar wasanninsa ta farko.

Dan wasan mai shekaru 35 a duniya ya zura kwallaye 18, tun bayan komawar sa kungiyar wasan kwallon kafa ta Mancester United, a lokacin da ya sauya sheka daga Paris Saint-Germain a wasannin bazara, kuma yanzu haka ma dai yana duba yiwuwar sauya sheka zuwa kungiyar Liverpool.

Dan wasan yana ji a ransa cewa ya riga ya samu nasara, kuma a yanzu zai iya komawa kungiyar wasan da yake hari ne da zummar lashe gasar wasanni ta Premier League.

Ibrahimovic ya shedawa manutd.com cewa, "ina yunkurin lashe lambar yabon ta Premier League. Na yi kokarin taimakawa kungiyar wasa na, kuma na yi bakin iyakar kokari na domin na zura kwallaye, na yi wasanni masu kyau, kuma na samar da damammaki ga abokan wasana. Idan har kuwa zan iya yin hakan, to hakika zan iya taimakawa ko wace kungiyar wasa.

"Lamarin iri daya ne, su ma suna taimaka mini iyakar yadda zasu iya. Ba ni da wani buri na kaina, domin na riga na cika shi. Bayan watanni uku a Ingila. Na yi galaba kan Ingila."

Ibrahimovic, ya yi amannar cewa, kungiyar wasan tayi nasara karkashin shugabancin Jose Mourinho tun shiga kakar wasannin da aka fara bugawa.

Ba a samu galaba kan United ba a cikin dukkanin wasanni 15, kuma sun yi nasarar a wasanninsu 9 na karshe a jere, amma har yanzu suna matsayi na 6 a teburin Premier League, kuma akwai tazarar maki 10 tsakanin kungiyar da Chelsea da ke kan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China