in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern Munich ta lashe kofin Telekom na kasar Jamus
2017-01-18 15:51:04 cri
A wasan karshe na gasar cin kofin Telekom ta shekarar 2017, wanda ya gudana a birnin Dusseldorf na kasar Jamus a kwanakin baya tsakanin kuloflikan Bayern Munich da Mainz, kungiyar Bayern ta doke Mainz da ci 2 da 1 ta kwallayen da 'yan wasan ta Franck Ribery da Javi Martinez suka ci.

Hakan ya kasance karo na 3 da fitacciyar kungiyar ta Bayern Munich ta lashe wannan kofi, wanda a baya a kan gudanar da gasar a lokacin zafi. A yayin wasan da aka buga, 'yan wasan Bayern Munich, karkashin jagorancin kocinsu Carlo Ancelotti, sun fara wasan da kyau, inda Franck Ribery ya yi amfani da damar da Thomas Mueller ya ba shi wajen cin kwallo farko, mintuna 4 bayan fara wasan. A hannu guda 'yan wasan Mainz sun ci gaba da buga kwallo cikin natsuwa, kuma bayan wasu mintuna 4, dan wasan kungiyar Andre Ramalho ya rama kwallon da Bayern ta ci su. Sai dai 'yan wasan Bayern Munich masu lakabin ''yan Bavaria', sun sake cin wata kwallon a minti na 11, haka kuma aka tashi babu karin kwallo.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China