Ofishin watsa labarai na shugaban kasar Rasha, ya sanar a jiya Alhamis cewa, shugaba Vładimir Putin, ya zanta da takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ta wayar tarho, inda shugabannin biyu suke ganin cewa, an kiyaye yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka kulla tsakanin gwamnatin kasar Syria da masu adawa da ita.
Baya ga haka, sanarwar ta ce, shugabannin biyu sun tsai da kudurin ci gaba da kokari, da nufin shirya taron samar da zaman lafiya a Syria, wanda za a yi a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan. (Bilkisu)