Ma'aikatar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya Alhamis, tana mai cewa, kungiyar OPCW ta fidda wani rahoto a bara, wanda ya nuna yadda sojojin gwamnatin Syriar suka kai farmaki har sau uku kan fararen hula da sinadarin Chlorine tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015. Hakan ne kuma ya sanya Amurka haramta wa wasu da ake zargi suna da hannu a aikata hakan, damar amfani da kadarorinsu a yankin Amurka, tare kuma da hana Amurkawa mu'ammalar cinikayya da su. (Bilkisu)