in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a zabi sabbin membobin kwamitin kungiyar AU a gun taron kolin kungiyar
2017-01-23 10:41:39 cri
An bude taron kolin kungiyar AU karo na 28 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a ranar 22 ga watan nan, inda a yayin taron za a zabi sabbin membobin kwamitin gudanarwar kungiyar.

Taron wanda zai wakana har zuwa ranar 31 ga wata, zai kunshi tarukan kwamitin zaunannun wakilan kungiyar, da na kwamitin gudanarwar, da kuma taron shugabanni da kusoshi.

Za a gudanar da taron kolin shugabanni da kusoshi a ranar 30 zuwa 31 ga wannan wata, inda za a tattauna, tare da tsaida kudurin warware matsalolin da ake fuskanta yayain da ake bunkasa nahiyar Afirka.

Kaza lika a gun taron, za a zabi sabbin mambobin kwamitin kungiyar AU, ciki har da shugaba, da mataimakin shugaba, da kuma membobin kwamitin su 8.

Shugaban kwamitin kungiyar AU shi ke da alhakin sa kaimi ga bunkasa nahiyar Afirka bisa tsarin bai daya, da gudanar da ajandar baiwa mata iko, da shirin bunkasa Afirka nan da shekarar 2063, da kuma shirin raya Afirka cikin wadata.

Za a tattauna yadda za a sa kaimi ga gina yankin ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afirka, don inganta musayar kayayyaki, da hidima a tsakanin kasashen Afirka. Kana za a tattauna game da izinin shiga kungiyar AU da kasar Morocco ta nema. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China