Madam Zuma ta kuma yi kira ga al'ummar Afirka, da su zama tsintsiya madaurinki daya, don dorawa a kan kokarin da ake na samarwa nahiyar kyakkyawar makoma..
Madam Zuma ta ce, nahiyar Afirka ba nahiya ce marar makoma mai haske ba, sannan bai kamata a ce ita ce ke kawo tsaiko ga ci gaban al'ummomin duk duniya ba a karni na 21.
Kasashen Afirka daban-daban za su yi tsayin daka wajen neman ci gaba mai dorewa, kuma ba za su amince da duk wani nau'i na nuna yatsa da kasashen yammacin duniya suka yi musu ba.
Don haka, ya zama dole kungiyar AU ta dogaro da kanta wajen samun ci gaba, da shawo kan matsalar karancin kudin tallafi.
Har wa yau, Madam Dlamini-Zuma ta ce, akwai alaka ta kut da kut tsakanin al'ummar kasashen Afirka, a don haka ya zama wajibi kasashen Afirka su gaggauta kafa kasuwa ta bai daya, tare da raya muhimman ababen more rayuwar jama'a, ta yadda za su samu ci gaba kafada da kafada.(Murtala Zhang)