Kwamishinan kungiyar AU mai kula da harkokin tsaro da zaman lafiya Smail Chergui, ya ce AU za ta ci gaba da goyon bayan yakin da ake yi da kungiyar nan ta Boko Haram, karkashin tawagar hadin gwiwar dakarun wasu kasashen yammacin Afirka ko MNJTF a takaice. Mr Chergui ya bayyana hakan ne yayin wani taron manyan dakarun sojojin tawagar wanda ya gudana jiya Alhamis.
Wata sanarwa da aka fitar bayan taron, ta nuna cewa mahalartan sa sun maida hankali ga tattauna yanayin tsaro da ake ciki game da ayyukan tawagar, da ma sauran muhimman hanyoyin bunkasa ayyukan tawagar.