in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun AU sun kashe mayakan Al-Shabaab 12 a Somaliya
2016-11-16 19:22:53 cri
Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa a kwanaki biyu da suka gabata, dakarun kungiyar tarayyar Afirka da ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Somaliya(AMISON) sun yi nasarar kashe mayakan kungiyar Al-Shabaab 12 tare da kwace wani gari da ke kudancin kasar.

Wata sanarwa da tawagar ta AMISON ta rabawa manema labarai a yau Laraba ta bayyana cewa, dakarun nata tare da hadin gwiwar sojojin gwamnatin Somaliya ne suka kashe mayakan, kana suka jikkata wasu 14 baya ga tarin makamai da suka kwace, a wani kwanton bauna da suka yiwa mayakan na Al-Shabaab, a lokacin da suke kokarin shiga gundumar Barire da ke yankin Lower Shabelle a ranar Litinin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China