Taron na kwanaki biyu, ana gudanar da shi ne a hedkwatar kungiyar ta AU dake Addis Ababa na kasar Habasha, kuma ya samu halartar ministocin harkokin wajen kasashen na AU.
A jawabinta na bude taron, Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar hukumar zartaswar kungiyar ta AU, ta bukaci kasashe mambobin kungiyar, da masu ruwa da tsaki dasu taka muhimmiyar rawa wajen cimma aiwatar da shirin muradin cigaban nahiyar nan shekarar 2063.
Shugabar ta AU, ta jaddada muhimmancin hako albarkatun kasa da Allah ya huwacewa nahiyar wajen samar da ayyukan yi ga jama'ar nahiyar, da bunkasa cigaban masana'antu, da samar da abinci da kuma ingantaccen cigaba a nahiyar baki daya.
Ministan harkokin wajen kasar Habasha Workneh Gebeyehu, yace taron ministocin harkokin wajen kasashen wata babbar dama ce da za ta baiwa kasashen mambobin kungiyar ta AU damar nazartar muhimman batutuwa da suka shafi cigaban nahiyar.