Shugaba Jammeh ya shaidawa 'yan kasar cewa, sashi na 34 na kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi ikon ayyana dokar ta baci, domin hana barkewar tashin hankali wanda ka iya kaiwa ga karya doka da oda.
Jim kadan da sanar da wannan doka, sai majalisar dokokin kasar wadda jam'iyyar Jammeh ke da rinjaye ta kada kuri'ar amincewa na bai daya da wannan doka.
Sai dai kuma dokar ta bacin tana zuwa ne a dai-dai lokacin da kimanin ministoci 8 da ke gwammatin Jammeh suka ajiye mukamansu.
Tun a ranar 9 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ce, kasar ta Gambia ta fada rikicin siyasa, lokacin da shugaba Jammeh ya amince da kayen da ya sha a zaben ranar 1 ga watan Disamban. Daga bisani kuma ya canja ra'ayinsa. (Ibrahim)