in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata samarwa manoman shiyyar arewa maso yammacin kasar tallafi
2016-11-03 10:55:11 cri
Kimanin manoman alkama da shinkafa 180,000 a jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya ne zasu ci gajiyar shirin bada tallafin noman rani na shekarar 2016/2017.

Ahmad Labaran, shine daraktan shirin sauya fasalin aikin gona ATA, ya sanar a Duste, babban birnin jihar cewa, gwamnati zata samar da tallafin irin shukawa, da taki, da magungunan ciyayi ga manoman.

A cewar Labaran, manoman alkama 90,000 ne zasu amfana da shirin wanda za'a fara a watan nan na Nuwamba na 2016, sannan manoman shinkafa dubu 90,000 ne zasu ci gajiyar shirin a farkon shekara ta 2017.

Daraktan ya kara da cewa, kowane manomi zai samu buhhunan taki 2 samfurin NPK da samfurin Urea buhu 1.

Kana kowane manomin zai samu kilogram 50 na irin shukawa, da kuma magungunan ciyayi lita biyu da rabi.

Daraktan yace, alkama tana bukatar sanyi don haka yafi dacewa a shuka ta a tsakanin watannin Nuwamba zuwa Disamba, daga bisani kuma sai a shuka shinkafa a farkon shekarar 2017.

Sai dai ofishin gudanarwar shirin na ATA yace, zai shawarci gwamnati ta rage adadin manoman alkama ta kuma kara yawan manoman shinkafa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China