Ministan aikin gona na Najeriya Audu Ogbeh, ya ce gwamnatin kasar ta kuduri aniyar amfani da takin gargajiya don habaka aikin gona a kasar.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ministan ya ce, tuni gwamnatin kasar ta fara ba da muhimmanci a fannin aikin gona, inda za ta samar da muhimman kayayyakin aikin gona da suka hada da takin gargajiya da magungunan kashe kwari.
Ogbeh ya ce, "Za mu ba da muhimmanci wajen bunkasa aikin gona don ya kasance a matsayin babbar hanyar samar da karfin tattalin arziki na GDP a kasar, sannan ma'aikatar gona tana kokarin samar da kyakkyawan yanayi ga masu sha'awar zuba jari a fannin, ta yadda za su samu damar gudanar da harkokinsu cikin nasara."
Ya kara da cewa, wannan mataki zai tabbatar da aniyar gwamnati ta kokarin samar da hanyoyin samun kudaden shiga, da kuma inganta rayuwar al'ummar Najeriyar.(Ahmad Fagam)