in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron karawa juna sani kan harkokin noma da masana'antu tsakanin Sin da Afirka a Afirka ta Kudu
2016-11-10 10:12:29 cri
Jiya Laraba, aka bude taron karawa juna sani kan harkokin noma na zamani da masana'antu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a babban birnin siyasa na kasar Afirka ta Kudu, watau Pretoria.

Jakadan kasar Sin dake kasar Afirka ta Kudu Tian Xuejun, ya halarci bikin bude taron, inda a jawabinsa ya bayyana cewa, ana fatan ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka gaba cikin yanayi mai kyau, ta yadda za a kawar da rashin fahimtar da wasu kasashen duniya suke yiwa hadin gwiwar Sin da Afirka.

A nasa bangare, mataimakin minista a fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu Buti Manamela, ya ce, yana sa ran za a ci gaba da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasarsa bisa ka'idar cin moriyar juna, kamar neman dawwamamman ci gaba tare, tunkarar sauyin yanayi cikin hadin gwiwa, da kuma karin ba da horo ga masana a kasashen Afirka a fannin kiyaye muhalli da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China