Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, za ta kara adadin kamfanonin sarrafa shinkafa domin cimma burin da kasar ke da shi na samar da shinkafa a cikin gidan nan da shekarar 2018.
Ministan noma da raya karkara na Najeriyar Audu Ogbeh, ya tabbatar da hakan ga 'yan jaridu a Abuja cewa, tuni gwamnatin kasar ta fara shirye shiryen samar da karin kamfanonin sarrafa shinkafa guda 40 domin cimma wannan buri.
A cewar Ogbeh, manufar shirin Najeriyar na inganta kamfanonin sarrafa shinkafa ita ce, domin samar da kasuwanni na cikin gidan da kasashen ketare ga manoman kasar, da kuma ba da karin damammaki domin habaka harkar noma a kasar.(Ahmad Fagam)