in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya: Sama da kashi casa'in na masu dauke da cutar kanjamau a jihar Akwa Ibom ba sa karbar magani
2017-01-21 12:31:40 cri

Wani jami'i a Nijeriya, ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, daga cikin mutane sama da dubu dari uku da hudu dake dauke da cutar kanjamau a jihar Akwa Ibom mai arzikin man fetur, dubu ashirin da hudu ne kadai ke karbar magani da shawarwari.

Manajan shirin yaki da cutar kanjamau da kula da masu dauke da ita na jihar Akwa Ibom, Nkereuwem Etok ne ya bayyana haka, lokacin da yake gabatar da rahoto game da yanayin da cutar ke ciki, yayin babban taro kan cutar kanjamau na bana da ya gudana a Uyo babban birnin jihar.

Etok ya bayyana rashin samun isashen tallafin kudi daga gwamnatin jihar da ayyukan kungiyoyin addini masu ikirarin suna da maganin cutar a matsayin kalubalen da shirin ke fuskanta.

Ya kuma koka kan yadda a koda yaushe, jihar ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, yana mai bayanin cewa, ko a kididdigar da aka yi a shekarar 2014, jihar ta dauki kashi 10.8 cikin dari.

Taken taron na bana shi ne 'cutar kanjamau a jihar Akwa Ibom, na tasiri ga makomarmu'.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China