in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rage farashin maganin Sida don a samu karin jama'a da za su amfana, in ji UNDP
2015-12-03 10:38:15 cri

Hukumar MDD ta ayyukan ci gaba wato UNDP ta ce, rage kudin magungunan kwayoyin cutar HIV zai sa mutane da dama su fara karban maganin da zai kara musu kwarin jiki.

A cikin sanarwar da aka fitar don bikin ranar cutar Sida ta duniya da aka yi a ranar 1 ga watan nan, hukumar UNDP ta ce, farashin magungunan kwayoyin HIV da kuma na cutar Sida, ana ta rage shi a cikin shekarun da suka gabata, abin da ya sa mutane da dama suka samu amfana daga hakan.

A shekara ta 2000, magungunan kwayoyin HIV da na cutar Sida ya kai fiye da dala 10,000 ga ko wane mara lafiya duk shekara. A cikin wata shekara kuma gaba daya farashin magungunan ya yi kasa bayan da masana'antu hada magungunan suka fara hadawa a farashin dalar 350 duk shekara ga mutun daya, ta haka farashin ya ci gaba da yin kasa har ya koma dala 150 ga mutum daya, in ji bayanin da ke dauke a ciki sanarwar da aka fitar a Lusaka, babban birnin kasar Zambiya.

A cewar sanarwar, wannan sauyin na farashi ya saka dunbin mutane masu dauke da kwayoyin cutar ko ma cutar gaba daya su miliyan 15.8 samun magani wadanda suka fi na shekaru 15 da suka wuce da mutane 700,000 kadai suka iya samun maganin a cikin shekara 1.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China