in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAIDS na tallafawa Kamaru domin hana yaduwar kanjamau
2015-06-02 11:12:03 cri

Darektan zartaswa na hukumar UNAIDS, mista Michel Sidibe, dake ziyarar aiki a kasar Kamaru, ya samu tattaunawa tare da faraministan kasar Philemon Yang a ranar Litinin a birnin Yaounde tare da kuma sabinta tallafin hukumarsa domin hana yaduwar ciwon kanjamau a kasar Kamaru, inda ma'aunin yaduwar wannan cuta ya ke kashi 4,3 cikin 100, kuma mafi tada hankali a yammacin Afrika da tsakiya.

Kafin 'yan shekarun da suka gabata, muna da kashi 14 cikin 100 na mahaifiya dake dauke da wannan cuta, na iyar samun ayyukan ba da kariya, domin ganin yaran da suke aifuwa ba su kamu da Sida ba. A yanzu muna da kashi 64 cikin 100.

Gwamnatin Kamaru ta kara kason kudi da kashi 2 cikin 100 kawai a shekarar 2009 zuwa kashi 25 cikin 100 a cikin yakin da take da Sida, in ji mista Sidibe

Ministan kiwon lafiyar kasar Kamaru, mista Andre Mama Fouda da yake amfani da hasashen UNAIDS ya bayyana gamsuwarsa kan kasarsa dake cikin jerin kasashen Afrika 22 inda sabon adadin kamuwa da kanjamu ya ragu da kashi 24 cikin 100. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China