Mista Rhodes ya shaidawa taron manema labarai cewa, manufar kasar Sin daya tilo a duniya, shi ne babban tushen raya huldar jakadanci tsakanin Amurka da Sin. Haka kuma kasar Sin ba za ta yi shawarwari da kowa ba a kan wannan manufa. Duk wani yunkuri na tayar da wannan batu, zai kawo mummunar illa ga dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, kuma babu wani bangare da zai amfana.
A wani labarin kuma, yayin zantawarsa da kafofin watsa labarai kwanakin baya, shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce manufar kasar Sin daya tak a duniya, yana daga cikin jerin abubuwan da za'a tattauna a kai. Game da furucinsa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mista Lu Kang ya ce, manufar kasar Sin daya tak a duniya, tushen siyasa ne na raya huldar Sin da Amurka, saboda haka, babu yadda za'a yi shawarwari a kansa. Lu kuma ya bukaci bangaren Amurka da ya girmama alkawarin da gwamnatocin Amurka daban-daban suka dauka, da daidaita batun yankin Taiwan ta hanyar da ta dace.(Murtala Zhang)