in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Duniya na sane da masu baiwa kasuwannin su kariya
2017-01-19 19:31:53 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a birnin Beijing a yau Alhamis cewa, a halin yanzu, kowa na sane da ko su waye ke gudanar da ra'ayin bada kariya ga cinikayyar su.

Kalaman na ta, na zuwa ne bayan da wanda ake sa ran nadawa a matsayin ministan harkokin ciniki na kasar Amurka Wilbur Ross, ya yi wani tsokaci a zaman majalisar dattijan Amurka domin tabbatar da nadin sa a jiya Laraba, inda ya bayyana cewa, Sin na aiwatar da manufar bada kariya ga cinikayyarta, wadda ko da yaushe ta kan furta bayanai kan yin ciniki maras shinge, maimakon daukar matakai a zahiri.

Game da wannan batu, Hua Chunying ta bayyana cewa, jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, yayin bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya wato Davos, ya jawo hankalin duniya sosai. Kaza lika bangarori daban daban na kasashen duniya, sun nuna yabo da amincewa da ra'ayoyin da ya gabatar a jawabin na sa, tare da ayyukan da kasar Sin take aiwatarwa.

Ta ce a halin yanzu, kowa ya san wane ne ke gudanar da ra'ayin bada kariya ga cinikayya da zuba jari, sabanin abun da Mr Ross ya bayyana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China