in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da kasar Sin ta zuba a ketare ya karu da kashi sama da 40% a 2016
2017-01-16 20:41:07 cri

Alkaluman da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar a ranar Litinin din nan sun nuna cewa, kasar ta zuba jari ga kamfanonin ketare 7961, na kasashe da yankuna 164 a shekarar 2016, inda yawan kudin da ta zuba din ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 170. Kuma jimillar adadin ta karu da kashi 44.1% idan an kwatanta da na shekarar 2015.

Da yake karin haske game da wannan ci gaba, jami'i a ofishin dake lura da ayyukan hadin gwiwa, karkashin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Han Yong, ya ce yadda kasar Sin take kokarin hadin gwiwa da kasashen dake cikin shirin nan na "ziri daya da hanya daya" da aka shata a shekarar 2016 yana da burgewa sosai. Ya ce hakika kamfanonin kasar sun zuba jarin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 14.53, a kasashen dake cikin shirin nan na "ziri daya da hanya daya". (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China