in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaran duniya sun rubuta sharhi kan taron tattalin arzikin kasar Sin
2016-12-22 15:13:37 cri

Kafofin watsa labarai da masharhanta na kasa da kasa sun rubuta sharhi game da taron tattalin arziki wanda gwamnatin kasar Sin ta gudanar a kwanan baya, inda suka nuna cewa, yayin da tattalin arzikin duniya ke fama da rashin tabbas, tattalin arzikin kasar Sin kuma yana cikin wani sabon yanayi ne, wannan taron zai taimaka wajen tabbatar da bunkasar tattalin arziki ba tare da wata fargaba ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Rasha wato ITAR-TASS ya bayyana cewa, raya tattalin arziki cikin daidaito shi ne ginshikin shirin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin a shekara ta 2017.

Shi kuma shafin intanet na Jaridar Wallstreet Journal na kasar Amurka ya ruwaito wani labarin dake cewa, taron tattalin arzikin da gwamnatin kasar Sin ta gudanar ya nuna alkiblar bunkasar tattalin arzikin kasar a shekara mai zuwa, inda batun raya tattalin arzikin cikin daidaito da kwanciyar hankali ya kasance babban burin da ake fatan za a cimma a shekara ta 2017. Haka kuma taron ya yi alkawarin magance duk wani hadarin da za a gamuwa da shi a fannin hada-hadar kudi.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China