in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Sin zai iya karuwa da kashi 6.7 cikin 100 a 2016
2017-01-10 14:48:26 cri
A jiya Talata, babban jami'i mai kula da tsare tsaren tattalin arziki na kasar Sin ya bada kiyasin ci gaban tattalin arzikin kasar a shekarar 2016, inda ya nuna cewa zai iya kai kashi 6 da digo 7 cikin 100.

Xu Shaoshi, daraktan hukumar ci gaban kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya shedawa manema labaru cewa, kasar Sin wadda ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, ta samu karuwar alkaluman tattalin arziki a watanni tara na farkon shekarar da ta gabata.

Ya ce, tattalin arzikin kasar, zai haura Yuan trillion 70 kwatankwacin dalar Amurka triliyon 10.1, wanda ya karu da yuan triliyon 5, kuma wannan karuwa ita ce mafi girma da aka samu a tsakanin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki.

Mista Xu ya buga misali da alkaluman kididdiga wanda asusun bada lamini na kasa da kasa IMF ya bayar inda ya ce, kasar Sin ta ba da gudumawar maki 1.2 wato kwatankwacin kashi 30 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya a shekarar 2016 da ta gabata, yayin da Amurka ta ba da gudumawar 0.3 wato kasa da maki daya ke nan ga ci gaban tattalin arzikin duniyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China