Shirin ya kuma tanaji kokartawa wajen sanya mutane miliyan 50 su shiga cikin harkar kasuwanci ta yanar gizon. An ce shekaru 20 da suka gabata ya zuwa yanzu, kasar Sin ta zama kasuwar cinikayya ta yanar gizo mafiya girma da saurin bunkasuwa a duk duniya, wanda hakan ya taka rawar a-zo-a-gani a fannonin habaka tattalin arziki, da raya sana'o'in kirkire-kirkire, da kuma rage kangin talauci da sauransu.
Sai dai a daya hannun, kasuwar cinikayyar kasar Sin ta yanar gizo na fuskantar wasu matsaloli a halin yanzu, hakan ya sa gwamnatin kasar ta bullo da wannan muhimmin shiri, don jagorantar bunkasarta ta hanyar da ta dace.
Bugu da kari, wannan shiri ya fitar da manyan ayyukan da za'a gudanar yayin da ake kokarin raya wannan harka, ciki hadda, kyautata ingancin harkokin cinikayya ta yanar gizon, da kokarin hada kasuwar cinikayya ta yanar gizo da sana'o'in gargajiya, da kuma bunkasa wasu muhimman abubuwan dake kunshe cikin kasuwar cinikayya ta yanar gizo. Sauran sun hada da kyautata zaman rayuwar al'umma ta cinikayyar yanar gizo, da inganta yanayin sa ido kan harkokin kasuwar cinikayya ta yanar gizo ko Intanet. (Murtala Zhang)