in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afirka da su zuba jari a bangaren makamashi da ake sabuntawa
2017-01-20 10:42:11 cri
Masana a harkar makamashi sun yi kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su zuba jari a bangaren ayyukan samar da makamashi da ake sabuntawa, a matsayin wata hanyar da za ta samar da makoma mai haske ga nahiyar.

Babban sakataren kungiyar da ke rajin kare muhalli a nahiyar Afirka (PACJA) Mithika Mwenda ya ce lokaci ya yi da kasashen na Afirka za su koma ga amfani da makamashin da ake sabuntawa maimakon makamashin da ke gurbata muhalli. Ya ce, ta haka ne kadai nahiyar za ta magance kalubalen da take fuskanta a bangarorin muhalli da tattalin arziki.

Mwenda ya ce, a yayin taron yarjejeniyar sauyin yanayi da aka gudanar a shekarar 2015, kasashen Afirka sun nemi taimakon kudi da fasahohi daga kungiyoyin bayar da rance na kasa da kasa domin daukar nauyin ayyukan samar da makamashi da ake iya sabuntawa a nahiyar.

Ya ce, shugabannin nahiyar da masu ruwa da tsaki, masana da masu zuba jari, duk sun yi ittifakin cewa, akwai bukatar nahiyar Afirka ta daina amfani da makamashi mai gurbata muhalli, duba da makuden kudaden da ake kashewa da kuma tarin illolin da hakan ke haifarwa muhalli.

Yanzu haka dai, kasashen Afirka sun fara amfani da matakan inganta zuba jari da sauran kasashen duniya suka bullo da su a fannin makamashi mai tsafta, a wani mataki na cimma nasarar manufofin ci gaba mai dorewa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China